Daga Rakiya A. Muhammad
Kowace shekara, dimbin mutane a cikin miliyoyin, na fuskantar bakin ciki na cin zarafin jinsi ta hanyar jima’i a fadin duniya. Wadanan qididdiga ba kawai lambobi ba ne kawai abubuwa ne da suka wakilci wata rayuwar da ta samu canji har abada.
A cewar Matan Majalisar dinkin Duniya, kimanin mata miliyan 736, kusan zaya a cikin mutum uku sun fuskanci cin zarafi ko dai na jima’i, ko na azabtarwa a zahiri daga abokan zama ko duka biyun, aqalla sau daya a rayuwarsu.
An dade ana yin shiru kan lamarin, amma yanzu, wani sabon salo na wayewa da fafutuka ya fara kunno kai a garin Sokoto dake arewa maso yammacin Nijeriya.
Daina yi shuru zuwa fafutuka wata alama ce da ke nuna yadda al’ummar Sakkwato ke qara fahimta da kuma shigar da su wajen magance cin zarafi na jinsi, wanda ke ba da kyakyawan fata wajen yaqar wannan lamari mai yaduwa.
Dabi’ar ta muzgunawa na rikidewa zuwa muryoyi mai qarfi a jihar yayin da masu ruwa da tsaki daban-daban suka haxa kai don tunkarar wannan mugunyar barazana.
“Wani mutum da ban san shi ba ya farmake ni a cikin daji. Bayan faruwar lamarin, na yi jinkirin bayyanawa ’yan uwana tsawon makonni saboda fargabar tsangwama. Bayan sanar da iyayena, sai da na yi kwanaki kafin kafin na samu nutsuwa a cikin jama’a saboda damuwa da kunya,” in ji Rashida, wadda ta tsira daga Sakkwato ta Kudu.
“Duk da haka, na samu qwarin gwiwa sosai bayan da yi hulxa tare da sauran wadanda suka kubuta da kuma bayyana abubuwan da suka faru. Yanzu ina shiga cikin jama’a gami da hulda da abokai ba tare da tsoro ba, ganin cewa ba ni kadai ce nake fama da hakan ba. ”
Daukar matakin hadin kai
Bisa la’akari da halin da ake ciki, masu ruwa da tsaki a fadin jihar Sokoto sun haxa baki daya. Daga qungiyoyin sa-kai zuwa hukumomin gwamnati, yunqurin gamayya yana da matuqar muhimmanci.
Jihar ta samu goyon baya daga qungiyar EU-UN Spotlight Initiative, wadda aka qaddamar a Nijeriya a shekarar 2019 domin yaqi da cin zarafin mata da ‘yan mata.
Wani bincike da aka yi a kan ayyukan Spotlight Initiative a Sakkwato daga Maris 2020 zuwa Oktoba 2023 ya nuna cewa Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato ta aiwatar da dokar kare haqqin yara ta Jihar Sakkwato yadda ya kamata a ranar 11 ga Nuwamba, 2021, wadda daga baya Gwamnan Jihar Sakkwato ya amince da ita a ranar 22 ga Nuwamba. 2021. Bugu da qari, an kafa dokar hana cin zarafin mutane (VAPP) a watan Yuli. 2021.
A halin yanzu dai Sakkwato tana da cikakkiyar cibiya ta wadanda suka samu kubuta daga cin zarafin mata da aka fi sani da Nana Khadija. Kimanin qararraki na tashin hankali 1460 ne aka ba da rahoton, kuma dukkan su sun sami tallafi mai mahimmanci, gami da ayyukan jin dadin rayuwa, jinya, da walwalar jama’a. Daliban da ba sa zuwa makaranta 9,310 waxanda aka mayar da su makaranta an samu nasarar yaye su daga tsarin shirin bayar da Ilimi na ‘Second Chance Education Program scheme’ na Jiha.
Daga cikinsu, akwai mata 60 da maza da maza 75 da suka yi tsayin daka wajen yin gwagwarmayar yaqi da cin zarafin jinsi ta hanyar jima’i, tare da mai da hankali kan ingantattun hanyoyin sadarwa da bayar da rahoto game da abubuwan da suka shafi mata da ‘yan mata.
Wata wadda ta tsira ta ba da labarin yadda da ta samu injin niqa daga Ma’aikatar Harkokin Mata, komawa makaranta, da qwarewar sana’ar dinki, duk ta hanyar tawagar Ceto Qananan Yara da shirye-shirye daban-daban a qarqashin shirin yaqi da cin zarafin mata ta hanyar jima’i da kuma ba wa qananan yara kariya.
Tawagar ta hadu da duk masu ruwa da tsaki, gami da hukumomin gwamnati, jami’an tsaro, da qungiyoyin jama’a, don tallafa wa wadanda suka kuvuta ta hanyar tallafa musu daga masu rauni zuwa masu qarfi.
Da ta waiwaya a baya kuwa, ta tuna da bala’in da wani mutum ya jefa ta ciki ya kuma vace, ya bar ta cikin matsanancin hali.
Bayan ta shafe tsawon lokaci tana fama da baqin ciki na irin illolin da ke tattare da cutar da ita da ya yi, an aurar da ita tun tana ‘yar shekara 14 ga wani mutum mai mata da ‘ya’ya. Ya zalunce ta, wanda a qarshe lamarin ya kai ga rabuwar auren bayan shekara uku, hakan ya sa ta koma zama tare da iyayenta. A wannan lokacin ne ta gano shirin mayar da martani na SGBV a cikin jihar, wani sauyi da ya buxe mata sabbin damammaki.
“Tarihin Sakkwato game da cin zarafi da ya shafi jima’i (SGBV) mara kyau ya daxe,” in ji Rabiu Bello Gandi, Kodinetan Yaqi Da Cin Zarafi da Jinsi/Tawagar Bayar da Kariya ga Yara Qanna.
“Shekaru uku nan da suka gabata, Jihar Sokoto ba ta da dokar kare haqqin yara ko wata doka da ta haramta cin zarafin mutane; mun dogara ne kawai ga Dokar Penal Code, wanda ya qunshi wasu qananan abubuwa- tarar da ake sanyawa ta yi kaxan. Za ka iya samu an tara tarar Naira 30 da Naira 50 a cikin kundin hukunta manyan laifuka.”
“Duk da haka, godiya ga jajircewa daga gwamnati da qungiyoyin jama’a,” in ji shi, “Mun sami damar samar da dabarun wayar da kan jama’a, da bayar da shawarwari don jawo hankali kan gaskiya, cewa cin zarafi na jinsi yana qaruwa kuma yana buqatar a dauki matakin gaggawa.”
Gandi ya tunatar da cewa kafin waxannan dokoki, shari’o’i na qaruwa, amma mutane ba sa kai labari, inda a cikin shekaru huxun da suka gabata aka samu qararraki biyu kacal a faxin Jihar Sakkwato.
“Amma, ta hanyar haxa kai da qoqarin wayar da kan jama’a da gwamnati, mun samu gagarumar nasara ta hanyar horar da shugabannin gargajiya da na addini kan rigakafin da kuma mayar da martani ga cin zarafin mata, da kuma hanyoyin bayar da rahoto, tare da goyon bayan qungiyar Initiative Spotlight, “in ji shi.
“Tare da wannan yunquri, Jihar Sakkwato ta samu qararraki fiye da 1,500 na cin zarafi da suka shafi jinsi, ciki har da cin zarafi, sakaci, fyaxe, da luwadi.”
Ya bayyana cewa an gudanar da muhimman ayyuka dangane da hukunta waxanda suka aikata laifin.
“A halin yanzu, jihar na fuskantar shari’a sama da 70, wadanda har yanzu ake ci gaba da gudanar da su. 54 daga cikinsu a halin yanzu suna zaman gidan yari, kuma makonni biyu da suka wuce, mun sake samun wani hukuncin xaurin rai da rai, ”in ji shi.
“Yanzu mutane sun san inda za su kai rahoto, kuma jami’an tsaro sun samu horo kan bincike da kuma gurfanar da su.”
Nasarar Adalci: Samun Goyon Bayan Shari’a
Wakilci na shari’a na iya zama muhimmin al’amari ga wadanda suka tsira daga cin zarafi da suka danganci jinsi a cikin neman adalci. Lauyoyin Pro bono, irin su Barista Rashida Muhammad, suna sadaukar da lokacinsu da qwarewarsu don tabbatar da cewa wadanda abin ya shafa sun sami goyon bayan shari’a da suke buqata, tare da ba su damar yin la’akari tsarin shari’a.
Alqawarin su yana nuna mahimmancin saka hannun jari a cikin shari’o’in daidaikun mutane da fadada yaqi da GBV.
“Mun yi nisa a inda muke yanzu, ya fi inda muka fito. Na fara wannan tafiya ne a shekarar 2018. A wancan lokacin, ba mu samu mutane da yawa da suka fito don yin magana kan cin zarafin mata ba, kuma ba a samu isasshen wayar da kan jama’a ba,” in ji mai fafutukar kare haqqin bil’adama Rashida Muhammad.
“Mata da yawa ba su san haqqinsu da yadda za su kai rahoton damuwarsu ba. Duk da haka, zan iya amincewa da cewa muna ci gaba idan aka kwatanta da halin da muke ciki a baya. Yanzu, akwai ci gaba. Na farko, muna da kayan aikin doka a hannunmu.
Ta bayyana cewa, “2019, ba mu da wani abu da ake kira dokar VAPP, ba mu da wani abu da ake kira Dokar Kare Qananan Yara ‘Child Protection Law’ sannan kuma Dokar Penal Code ita ce tsohuwa. ”
“Tsakanin 2019 zuwa yau, muna da dokarmu ta Penal Code 2019, muna da tsarin shari’a na laifuka na 2019, muna da dokar hana cin zarafin mutane, da dokar kare haqqin yara, waxanda duk kayan aikin kwanan nan ne da aka kafa a Sakkwato.”
Ma’aikaciyar lauyoyin, wacce kuma ita ce shugabar qungiyar lauyoyin Nijeriya a Sakkwato, ta tuna cewa a lokacin da ta fara tafiya a shekarar 2019, mutane da dama sun fuskanci qalubale wajen bin diddigin lamarin.
“Na farko, ba su bayar da rahoton shari’ar ‘GBV’ ba; Idan muna da qarar cin zarafi 10 na mata, mutane biyu ko uku ne kawai za su bayar da rahoto, kuma ko da bayan sun bayar da rahoto, ba za su bi shi zuwa ga ma’ana ba, “in ji ta.
“Yanzu mun ga iyaye, har da maza, sun fito suna cewa an ci zarafin wannan matar kuma ta cancanci a yi mata adalci, kuma a shirye suke su bi ta har zuwa ga cimma matsaya.”
Har ila yau vangaren shari’a na Sakkwato yana samun ci gaba a yaqi da SGBV, a cewarta.
“A lokacin da muka fara, muna da alqali mace daya kacal; yanzu idan ka duba vangaren shari’a na Jihar Sakkwato muna da alqalai mata guda biyar. Wannan nadin na kwanan nan ya yi la’akari da kimanin alqalai mata guda uku domin a dunqule za mu samu alqalai mata takwas a ma’aikatar shari’a ta Jihar Sakkwato, babbar kotun Jihar Sakkwato,” in ji Barista Rashida.
“Lokacin da kuka ziyarci kotun majistare, za ku ga alqalai mata da yawa sun hallara. Daya daga cikin dalilan da ya sa galibin wadannan iyaye ko matan ba sa son bin diddigin shari’o’insu ko kuma zuwa kotu shi ne saboda suna ganin tsarin bai san da kevantacciyar mata ba; misali, alqali namiji ne, lauyoyi maza ne, kowa da kowa.”
Yanzu, ta ce “Ko da a kotu za mu iya ganin cewa muna da wasu qararraki da aka gabatar da su zuwa ga ma’ana.”
Hakazalika, ta lura cewa hukumomin tsaro irin su ‘yan sanda da Civil Defence a yanzu suna da tebura na jinsi ko rukunin iyali saboda jerin horon da suka samu da kuma ci gaba a gudanar da bincike.
Masu Kula da Al’adu: Jagorancin Sauyin Cikin Gida
Shugabannin gargajiya suna tasiri sosai ga al’umma, suna aiki a matsayin masu kula da al’adu da dabi’u. A cikin yaqi da cin zarafi ‘GBV’, suna ci gaba don sake fasalin labarai da qalubalantar ayyuka masu cutarwa. Matsayinsu na musamman ya ba su damar cike givin da ke tsakanin qoqarin majalisar dokoki na zamani da kuma tushen al’adu mai zurfi, havaka sayayya a al’umma don canji.
Alhaji Sani Umar Jabbi, Sarkin Yaqi Gagi, shi ne Hakimin Gagi, kuma fitaccen shugaban gargajiya ne a yaqin da ake yi da SGBV a Sakkwato, wanda ke xauke da kyakkyawan fata. Qarfin gwiwar masu ruwa da tsaki da ingantaccen tsarin ba da amsa suna sake fasalin ra’a yi mara kyau na yammacin duniya, qalubalen da shi da wasu ke magana da qarfin hali.
“Muna faxakar da mutane game da samar da kayan aikin addini da ke nuna cewa Musulunci bai hana yaqi da cin zarafin jinsi ba, wanda ke goyon bayan adalci ga bil’adama da wanda ya tsira,” in ji shugaban gargajiya.
“Muna amfani da kayan aikin addini—jama’a, addu’o’in Musulmi, Sallar Juma’a, sauran bukukuwan addini da na zamantakewa, da kuma bukukuwa na duniya. Muna amfani da kowane dandalin tattaunawa don wayar da kan masu sauraro, samar da tarurruka na gari, samar da ra’ayi da kuma taron tawagar martani mai dorewa, da gudanar da tarurrukan da mataimakin gwamnan jihar ke jagoranta.”
Alhaji Sani Umar Jabbi ya qara da cewa a matsayinsu na sarakunan gargajiya su ne kan gaba wajen haxa kan al’umma don sauya al’adarsu da fahimtarsu. “Canza ra’ayi mara kyau ba zai yuwu ba tare da hadin gwiwar masu tsaron qofa ba,” in ji shi.
“Haxin gwiwar shugabannin gargajiya yana haifar da gagarumar nasara, yayin da muke aiki a matsayin masu kula da talakawa, da inganta alaqa tsakanin al’umma, gwamnati, da masu ba da ayyuka.”
Hadiza Shagari kwamishiniyar harkokin mata da yara ta Sakkwato ta bayyana fitattun nasarorin da jihar ta samu wajen samar da dokar hana cin zarafin yara (VAPP) da dokar kare haqqin masu buqata musamman.
Wadannan dokoki, in ji ta, sun inganta kariya da haqqoqin mata da qananan yara a jihar, wanda ke nuna wani gagarumin ci gaba a jajircewar jihar wajen kyautata rayuwarsu.
Ta qara tabbatar da cewa jihar ta jajirce wajen ganin ta tabbatar da ganin mata da ‘yan mata sun samu kulawar da ta dace ba tare da wani cikas ba, tare da taimaka musu a qoqarinsu na sake gina rayuwarsu biyo bayan abubuwan da suka faru da su.
Kwamishiniyar ta nanata jajircewar jihar wajen kawar da tashe-tashen hankula da munanan ayyuka da ake yi wa mata da yara.
Aikin Da Aka Sa Gaba
Duk da ci gaban da aka samu, akwai matsaloli masu yawa. Masu ruwa da tsakin sun bayyana cewa rashin isassun kudade na wurin matsuguni da Cibiyar Ba da Agajin Jima’i ya sa ma’aikata sukuni.
Sauran qalubalen sun hada da rashin isassun tallafin rayuwa ga waxanda suka tsira daga SGBV, qarancin tattalin arziƙin da ke aiki a zaman jawo GBV, da kuma kawo qarshen shari’o’i a tsakiyar zaman kotu saboda rashin samun waxanda suka tsira da danginsu a matsayin shaida.
Suna jaddada buqatar haxin kai don shawo kan sauran matsalolin da kuma haifar da gado na rashin haquri ga SGBV, da hangen nesa ga al’umma inda kowane mutum yana da aminci da girmamawa.